1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Dakatar da aikin agaji

July 6, 2020

An shiga rudani bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da duk ayyukan jin kai da ake yi ta hanyar amfani da jiragen sama masu saukar ungulu.

https://p.dw.com/p/3eruX
Nigeria Maiduguri Flüchtlingslager
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun dakatar da ayyukan agaji a NajeriyaHoto: Reuters/A. Akinleye

Matakin Majalisar Dinkin Duniyar na dakatar da kai agajin ya biyo bayan wani hari da mayakan Boko Haram su kai wa jirgin majalisar, a wani hari da su ka kai a Damasak da ke jihar Borno a karshen mako. Cikin wata sanarwar da ofishin majalisar mai kula da ayyukan jin kai a Najeriya ya aikewa manema labarai, ya nunar da cewa an samu asarar rayukan fararen hula biyu ciki har da yaro dan shekaru biyar yayin harin.

Tilas a kare rayukan jami'an agaji

Duk da dai ba wanda ya jikkata daga harin da aka kai wa jirgin da aka yi kuma jirgin ya sauka a Maiduguri lafiya. Babban jami'in majalisar mai kula da ayyukan jin kai a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar, Dr Edward Kallon ya ce ya zama dole su dakatar da ayyukan jiragen har sai sun zauna da hukumomin kasar, domin samun tabbatacin kariya daga irin wannan hari.

Nigeria | Niedergebrannte Fahrzeuge in Auno
Hare-haren Boko Haram na kamariHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Malam Modu Gamboru wani ma'aikacin agaji da wannan mataki ya shafi aikinsa, ya tabbatar da dakatar da ayyukan jiragen masu aikin jin kai. Yanzu haka dai ayyukan jin kai sun shiga halin tasku, sakamakon wannan mataki da Majalisar Dinkin Duniyar ta dauka. Tuni dai kungiyoyin fararen hula a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar, suka fara bayyana damuwa kan abin da ya faru da ya kai ga dakatar da ayyukan jin kan.

Ma'aikatan agaji cikin garari

Masu fashin baki kan harkokin yau da kullum sun bayyana cewa, ya kamata hukumomi su dauki matakin gaggawa domin ganin an dawo da ayyukan agajin. Yanzu haka akwai ma'aikatan jin kai da mayakan Boko Haram suka kama a kan hanyoyinsu na zuwa wuraren aiki suke kuma yin garkuwa da su tare da barazanar halaka su, abin da ya sa yawancin ma'aikatan jin kai suka daina bin hanyoyi sai jirgin sama mai saukar ungulu, sai kuma ga shi a hakan ma ba su tsira ba.