1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure magajin garin Santanbul

Ramatu Garba Baba
December 14, 2022

Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara biyu da watanni takwas kan magajin garin birnin Santanbul a bisa laifin zagin jami'an hukumar zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4Kwtj
Magajin garin Santanbul Ekrem Imamoglu
Magajin garin Santanbul Ekrem ImamogluHoto: Burak Kara/Getty Images

Wata kotu a Turkiya ta zartas da hukuncin dauri na sama da shekaru biyu kan Ekrem Imamoglu, wanda shi ne magajin garin Santanbul kuma madugun jam'iyyar adawar kasar ta RPP, har wa yau kotun ta haramta masa shiga duk wasu lamura na siyasa. An yanke masa hukuncin ne, bayan samun shi da laifin zagi da kuma bata sunan wasu manyan jami'an hukumar zaben kasar.

A martanin da ya mayar bayan hukuncin kotun mai cike da ce-ce-ku-ce Imamoglu ya ce, yarfen siyasa ne don hukuncin ya sabawa dokar kasar. Masu sukar hukuncin suma sun danganta shi da kokarin kawar da wanda ya kasance babban mai adawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan da gwamnatinsa, ganin hukuncin kotun ka iya sa ya rasa mukaminsa na magajin garin Santanbul.