1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara jigilar mahajjatan Nijar bayan jinkiri

Abdullahi Mammane Amadou/ A'RHAugust 26, 2016

Bayan tsawon lokaci na samun jinkiri a wannan Lahadin ce aka fara jigilar Alhazai da ke niyar zuwa sauke farali daga Jamhuriyar Nijar zuwa kasa mai tsarki.

https://p.dw.com/p/1JqoI
Beginn Pilgerfahrt Hadsch in Mekka 01.10.2014
Hoto: Reuters/Muhammad Hamed

Mahajjatan jamhuriyar Nijar sun fara tashi zuwa kasar Saudiya biyo bayan dogon lokacin da aka dauka ba tare da fara kwasar maniyattan ba don sauke farali, wannan lamarin ya sanya dubban maniyatan kasar cikin zullumi duba da lokacin rufe birnin Madina na karatowa.

Kimanin mahajjata sama da 12,000 ne ake sa ran za su halarci kasa mai tsarki, sai dai maniyatan na takaici na jinkiri. A tun ranar 16 ga watan Augusta ne ake sa ran fara jigilar maniyyatan amma har yanzu su na jiran tsammani a wasu sansanonin da aka tanadar musu. Kungiyoyin sufrin mahajjatan Nijar dai na zargin kamfanin alhazzai da haddasa matsalar duba da rashin basu sararin magana da masu jirgi kai tsaye don kwasar alhazan.

Pilgerinnen aus Nigeria in Saudi Arabien
Mahjjata Afirka kan fuskanci tsaiko na jigilarsu zuwa kasa mai tsarkiHoto: DW

Sai dai tuni 'yan rajin kare hakin dan Adam ke sukar lamirin hukumar alhazan kasar, amma kawo yanzu babu martani daga hukumar alhazan a kan wannan batu. Bayan bayar da rahoton soma jigilar aikin hajjin na mahajjatan Nijar a ranar 16 ga wannan watan da aka dage, hukumar ta kara bayyana ranar 28 a matsayin ranar da ake sa ran mahajjatan kasar za su su fara tashi zuwa birnin Madina ko da ya ke maniyatan na yi wa batun kallon tamkar na 'yan matan amarya ne kawai.