1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara sako fursunonin siyasa a Pakistan

Ibrahim SaniNovember 20, 2007
https://p.dw.com/p/CJUL

Mahukunta a Pakistan sun fara sako fursunonin siyasa da aka tsare, a lokacin zanga-zangar adawa da Gwamnati.Waɗanda aka sakin sun haɗar da Lauyoyi da kuma masu fafutikar kare haƙƙin Bil´adama.To amma ya zuwa yanzu, wasu daga cikin gagga-gaggan ´ Yan siyasa na ƙasar ciki har da Imran Khan na ci gaba da kasancewa a hannun Jami´an tsaron. Shugaba Pavez Musharraf, wanda ke shirin balaguro izuwa Saudiya, ya jaddada ci gaba da kasancewar dokar ta ɓacin daya ƙaƙabawa ƙasar. A cewar shugaba Musharraf, dokar za ta taimaka wajen gudanar da zaɓe mai tsafta a ƙasar.Tuni ´Yan adawa na ƙasar su ka yi watsi da wannan shiri,da cewa babu abinda zai haifar illa koma baya ga tafarki na Dimokruɗiyya da ƙasar ta sa a gaba.