Sakamakon farko na zaben Gambiya
December 2, 2016Sakamakon farko na zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Gambiya na nuni da cewa jagoran 'yan adawa Adama Barrow ya shiga gaban Shugaba Yahya Jammeh, bayan da aka kirga kimanin kaso 75 cikin 100 na daukacin kuri'un da aka kada.
An fara dakon sakamakon zaben bayan kammala kda kuri'a a ranar Alhamis daya ga watan Disamabra da muke ciki, inda Shugaba Yahya Jammeh ke fatan ci gaba da fadada mulkinsa bayan shafe shekaru 22 kan madafun iko. Hukumomi sun katse hanyoyin sadarwa na wayar tarho da kafar intanet bisa dalilan tsaro a cewar ministan yada labarai Sherif Bojang. Tuni kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka soki matakin gwamnati na katse hanyoyin sadarwa, inda a hannu guda kuma tuni mahukuntan kasar suka kara karfafa matakan tsaro.
Kimanin masu zabe dubu 900 da suka cancanci kada kuri'a ne suka kada kuri'unsu a zaben na ranar Alhamis, inda madugun 'yan adawa Adama Barrow ke zama babban mai kalubalantar Shugaba Yahya Jammeh wanda yake kan madafun iko tun shekarar 1994, bayan juyin mulkin sojoji, kuma ya lashe zabukan da aka yi a baya a kasar ta Gambiya da ke yankin yammacin Afirka.