An fara sayar da hannayan jari na Facebook
May 19, 2012Talla
An buɗe kasuwar sayar da hannayan jari na Facebook a Amurka inda masu zuba jari suka yi cikar kwari a kasuwannin bayan da shugaban kamfanin ya buga ƙararrawar buɗe kasuwar tun daga jihar Kaliforniya.Lokaci kaɗan bayan an fara sayar da hannayan jarin farashin ya tashi da kimanin kashi 12 cikin 100,daga dala 38 zuwa dala 42 ko wane hannun jari.To amma daga bisannin frashin ya koma yada yake a da.Mutane kusan miliyan ɗari tara da rabi ne ke yin amfani da shafin a duniya, wanda a yanzu da wannan frashin darajasa za ta ƙaru da biliyan 104 a cikin shekaru takwas da kafamin ya fara aiki.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar