An fara tattauna rikicin Siriya a Geneva
January 25, 2014Talla
Ɓangarorin biyu waɗanda suka shiga zauren taron MDD na Geneva a ƙofofi daban-daban, sun kwashe wani ɗan takaitaccen lokaci suna sauraron jawabin Lakdar Brahimi a kan yunƙurin neman sulhu a rikicin na Siriya ba tare da yi wa juna magana ba.
Yanzu haka dai sassan biyu na can sun shiga tattaunawa batuttuwa mafi mahimmanci kamar yadda wani mai sulhuntawa na 'yan adawa Anas Albade ya sanar. Ya ce : '' Maganar dakatar da buɗe wuta da kuma kai kayan agaji a garin Homs na daga cikin batutuwan da muke ƙoƙarin ganin an samu daidaituwa a kansu kafin a kai ga maganar fursunonin siyasa da waɗanda aka sace.''
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba