1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fito da littafin bankada kan Trump

Zulaiha Abubakar
January 5, 2018

Tsohon na hannun daman shugaban kasar Amirka Donald Trump ya wallafa wani littafin da ke samun karbuwa yanzu a fadin Amirka saboda bayyana rauni da gazawar shugaba Trump.

https://p.dw.com/p/2qPzV
Steve Bannon
Steve BannonHoto: picture-alliance/AP Photo/B. Anderson

Littafin da aka kaddamar a wannan Juma'a, mai dauke da tonon sililin  shekara guda ta mulkin shugaba Donald Trump ya bayyana rauni da kuma gazawar shugaban a rubuce, koda yake Mr Trump ya mayar da martani ta shafinsa na Twitter in da ya bayyana littafin da cewa cike yake da karairayi da kuma rashin fahimta da kuma bayanan da basu da tushe. Tun da fari dai sai da Lauyan Donald Trump ya bukaci mawallafin littafin da ya dakatar da kaddamarwar, sai dai Steve Bannon ya sauya ranar kaddamar da littafin zuwa Juma'ar.

 A nata bangaren kakakin fadar White House, Sarah Huckabee Sanders, ta yi Allah wadai da wannan lamari inda ta kara da cewar ko a baya Steve Bannon yafi sadaukar da lokacin sa wajen ganawa da 'yan jaridu maimakon da shugaba Trump. Yanzu dai dubban Amirkawa ne ke tururuwar sayen wannan littafi, koda yake Lauyan shugaba Trump ya ce za su dauki mataki na shari'a.