1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano kura-kurai a tsarin zaben Jamus

Gazali Abdou Tasawa
September 7, 2017

Wasu kwararru a harkar konfuta sun bankado wasu manyan kura-kurai a cikin manhajar da za a amfani da ita wajen tattara sakamakon zaben wanda za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Satumba. 

https://p.dw.com/p/2jWnQ
Veranstaltung in Berlin, Bundesversammlung des Bundes der Vertriebenen und die Wahl des neuen Präsidiums
Hoto: DW

A kasar Jamus a daidai lokacin da ya rage kasa da makonni uku a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, wasu kwararru a harkar konfuta sun bankado wasu manyan kura-kurai a cikin manhajar da za a amfani da ita wajen rijistan sakamakon zaben wanda za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Satumba. 

Jaridar die Zeit ta kasar ta jamus mai fita mako mako wacce ta ruwaito wannan labari ta ce kungiyar kwararrun a harkar konfutar ta CCC wace ke daya daga cikin Kungiyoyin masu kutsen satar bayanai ta hanyar konfuta mafi tasiri a Turai ta gano cewa babu wani mataki na kariya ko na tabbatar da sahihancin alkalumma da aka tanada daga lokacin aiko da sakamakon zabe daga kananan hukumomi zuwa cibiyar hukumar zaben ta kasa. 

Kuma hakan na iya bayar da damar yin kutse da juya sakamakon zaben daga yadda yake a hakikanin gaskiya.