1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Tashin hankali na karuwa a Afghanistan

Suleiman Babayo
April 13, 2021

Hare-haren tsageru masu dauke da makamai sun janyo mutuwar fiye da jami'an tsaron Afghanistan 20 cikin kwana daya.

https://p.dw.com/p/3rwrR
Afghanistan Autobombenanschlag in Herat
Hoto: Shoib Tanha/DW

Fiye da jami'an tsaron kasar Afghanistan 20 sun halaka cikin kwana guda sakamakon hare-hare cikin manyan larduna hudu na kasar. Hukumomi sun ce daga ciki akwai sojoji 10 da suka rasa rayukansu bisa harin 'yan kungiyar Taliban masu dauke da makamai.

Hare-haren na zuwa lokacin da Shugaba Ashraf Ghani ya bukaci 'yan Taliban su tsagaita wuta na rikicin da ke faruwa saboda azumin watan Ramadan da Musulmai suka fara a sassan duniya. Kasar ta Afghanistan tana ci gaba da samun kanta cikin tashe-tashe hankula masu nasaba da tsagerun Taliban da sauran kungiyoyi masu masu kaifin kishin Islama.