1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojoji sun kai farmaki kan 'yan ta'adda a Najeriya

July 2, 2024

Sojojin hadin guiwa na kasashen gabar tafkin Chadi sun halaka ‘yan ta'adda 70 da lalata sansanonin mayakan ISWAP a jihar Borno kwana biyu bayan hare-haren kunar bakin wake kan fararen hula a garin Gwoza a kudancin jihar.

https://p.dw.com/p/4hmzT
Najeriya | Sojojin Najeriya
Sojojin NajeriyaHoto: AFP/Getty Images

Tun bayan da wasu mata ‘yan kunar bakin wake su ka kai wasu munanan hare-hare a Karamar hukumar Gwoza inda su ka halla mutane 32 jami'an tsaro su ka bazama domin farauto wadan ake zargin su na da hannun a wadan hare-hare. An yi imanin cewa wadan su ka kitsa wadan hare-hare na boye a wasu sansanonin da ke kan iyoyin kasashen Najeriya da Kamaru da ke bakin gabar tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa da ke zama babbar tunga da mayakan ke da sansanoninsu.

Karin Bayani: Hare-haren kunar baklin wake sun salwantar da rayuka a Najeriya

'Yan ta'adda a jihar Borno da ke Najeriya
'Yan ta'adda a jihar Borno da ke NajeriyaHoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Da wannan yunkuri ne Sojojin da ke aiki karkashin rundunar ta hadin guiwar da kasashen da ke bakin gabar tafkin Chadi suka samu nasarar halaka mayakan Boko Haram tare da lalata manyan sansanoninsu guda biyar a garuruwan da ke kan iyakokin kasashen Najeriya da Kamaru. Yayin da mutanen wannan yankin suka bayyana farin ciki da wannan nasara sun kuma bukaci rundunar tsaro da kara kaimi wajen zakulo sansanonin ‘yan ta'adda domin murkushe su don magance hare-hare da ke neman mayar da hannun agogo baya.

Jami'an tsaro na ganin irin wannan hare-hare na sari ka noke da mayakan ke kai wa na da alaka da matsin lamba da sojojin suka yi wa mayakan da kuma sakin jiki da aka yi na ganin an samu zaman lafiya. Wannan nasara da rundunar sojojin hadin guiwa suka samu dai wani mataki ne da ake ganin tauna tsakuwa domin a bai wa aya tsoro biyo bayan sabunta hare-hare da bangarorin mayakan Boko Haram ke kai wa a ‘yan kwanakin nan.