1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hallaka wasu 'yan bindiga a Kenya

June 19, 2014

Dakarun Kenya sun kashe mutane biyar da ake zargi na da hannu a wani harin kisan gilla da aka a yankin gabar tekun kasar.

https://p.dw.com/p/1CMVR
Mpeketoni Kenia Anschlag Massaker
Hoto: Reuters

Dakarun tsaron Kenya sun kashe mutane biyar da ake zargi suna da hannu a kisan gillan da aka yi farkon wannan mako a garin Mpeketoni na gabar teku. A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Twitter ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce an harbe mutanen ne lokacin da suka yi kokarin tserewa kuma an gano bindigogi uku samfurin AK-47 da kuma albarusai a wurin da lamarin ya auku. An dai girke sojojin Kenya a yankin bayan kisan gillan na ranar Lahadi inda aka kashe mutane kimanin 50 a garin na Mpeketoni da kuma wani kauye da ke kusa inda aka kashe mutum tara. Kungiyar Al-Shabaab ta kasar Somaliya ta dauki alhakin kai hare-haren, amma shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya zargi kungiyoyin siyasa na yankin da kuma wasu bata-gari da aikata wannan ta'asa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman