Nijar: Hana rantsuwa da Al-Qur'ani
January 13, 2021Tuni dai bangarorin siyasar kasar suka soma mayar da martani a kan wannan mataki da cikin wani sako da ministan cikin gida ya aikawa gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi na Nijar, ya umarce su da su dauki matakin dakatar da wannan al'ada ta kewaya laya ko Al-Qur'ani da wasu 'yan kasar ke yi kamar yadda aka gani musamman a lokacin zaben shugaban kasa zagayen farko, inda magoya bayan 'yan adawa suka yi ta kewaya layar da nufin hana magudin zabe. Ofishin ministan cikin gidan ya ce al'adar gitta alkur'anin ta saba wa kudiri mai lamba takwas na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya rarrabe addini da siyasa.
Da yake mayar da martani kan wannan mataki, Alhaji Dudu Rahama kakakin kawancen jam'iyyun adawa cewa ya yi al'adar sanya Al-Qur'anin ba ta sabawa kowacce irin dokar kundin tsarin mulkin kasar na Nijar ba. Tosai dai Malam Assoumana Mahamadou kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki, na ganin matakin gwamnatin ya yi daidai domin al'adar kewaya layar wasa ne da Al-Qur'ani.
Karin Bayani: Fara sanar da sakamakon zabe a Nijar
A hannu guda kuma a karon farko a Jamhuriyar ta Nijar, kananan jam'iyyu na neman kasancewa raba gardama a zaben shugaban kasa zagaye na biyu, domin kuwa a daidai lokacin da ake kallon jam'iyyar MNSD Nasara wacce ta samu sama da kaso takwas cikin dari a zaben da ya gabata da kuma jam'iyyar MPR Jamhuriya wacce ta samu sama da kaso bakwai cikin dari, a matsayin masu raba gardama a tsakanin 'yan takara a zaben shugaban kasa zagaye na biyu, sai gashi kamar daga sama wasu tsofaffin 'yan takara 10 wadanda a jumulce ke da sama da kaso tara cikin 100 na neman zama kan gaba cikin jam'iyyun da ka iya yin tasiri a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a gudanar a ranar 21 ga watan Fabarairu mai zuwa.