1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An jikata 'yan aikin agaji a Siriya

February 8, 2014

Masu aikin agajin jinkai hudu sun samu raunika sakamakon harin da aka kai musu cikin yankin Homs mai fama da tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/1B5aF
Hoto: Reuters/Thaer Al Khalidiya

Kafofin yada labarai na gwamnatin kasar Siriya sun ruwaito cewa an jikata ma'aikatan agaji hudu na kungiyar Red Crescent, lokacin da suke aikin jinkai cikin yankin Homs wanda ke hannu 'yan tawaye.

Sanarwar ta ce an bude wuta kan tawagar 'yan agajin. Ana ci gaba da samun tarnakin kai kayan agaji saboda yadda duk bangarorin ke zargi juna da saba yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla. Shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya da bangaren 'yan tawaye sun amince da wata tudun dafawa a karon farko yayin taron birnin Geneva, amma yanzu wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tana neman zama shiririta.

Masu fafutuka sun ce gwamnati ta cilla kimanin rokoki 11 cikin yankin da ke hannun 'yan tawayen.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal