An kai hari wata mujami'a a Turkiyya
January 28, 2024Ministan harkokin cikin gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya ya ce wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kaddamar da hari a wata mujami'ar Italiya da ke birnin Istanbul, inda mutum daya ya rasa ransa.
A cikin sanarwar da ministan ya fitar, ya ce maharan sanye da takunkumin rufe fuska sun kai harin ne da safiyar wannan Lahadi a Mujami'ar Santa Maria a lokacin da ake tsaka da gabatar da ibada.
A yayin da ya ke Allah wadai da harin, Yerlikaya ya ce, an fara gudanar da bincike kan hari kana mahukunta na aiki domin kama maharan. Kawo yanzu dai ba a san manufar kai harin ba.
A watan Disambar 2023 hukumomin tsaron Turkiyya suka kama mutum 32 da ake zargi suna da alaka da kungiyar IS da suke shirya kai hare-hare kan mujami'u da kuma offishin jakadancin Iraqi.