An kai mummunan hari cocin Koptik a Masar
April 9, 2017A kasar Masar wasu tagwayen hare-haren ta'addanci da aka kai a wasu Coci-Coci a birane biyu na kasar a wannan Lahadi sun yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 40. Gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa hari na farko an kai shi ne da misalin karfe goma na safiyar yau a Cocin Kiristoci mabiya darika Koptika na garin Tanta da ke a nisan kilomita 120 arewacin birnin Alkahira inda mutane akalla 25 suka rasu a yayin da wasu 78 suka ji rauni
Tashar talabijin ta Etra News mai zaman kanta a kasar ta Masar ta nuna cikin ginin Cocin da irin yadda jini ya fantsama ko ina a saman ginin dama yadda kujerun zama na cikin cocin suka kaca kaca
Hari na biyu wanda na kunar bakin wake ne an kai shi ne a Cocin birnin Alexandrie, inda ya zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwar mutane 11 a yayin da wasu 35 suka sami raunuka. Tuni dai Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare na wannan rana ta lahadi a kasar ta Masar.