Amrullah Saleh ya tsallake harin ta'addanci
September 9, 2020Mataimakin shugaban Afganistan Amrullah Saleh ya tsallake rijiya da baya amma an sami mutuwar mutum biyu tare da jikkatar wasu 12 daga cikin jami'an tsaronsa da sanyin safiyar wannan Laraba.
Har wayau an sami mutuwar fararen hula sama da 20 sannan wasu kimanin 50 sun jikkata a wajen da lamarin ya auku a cewar ma'aikatar lafiyar kasar.
Ya zuwa wannan lokacin babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari. Amma dai ana zargin 'yan kungiyar Taliban kasancewar Amrullah Saleh ya dade yana sukar lamirin ayyukan 'yan kungiyar.
Wannan harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon ci gaba da zaman sulhu da 'yan Taliban a birnin Doha na kasar Qatar.
Haka kuma a wannan Laraba shugaban Amirka Donald Trump ke shirin sanar da janye dakarun sojin kasarsa daga Afganistan kamar yadda yarjejeniyar da suka cimma da 'yan Taliban ta tanada.