1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama daruruwan masu bore a kasar Kenya

Binta Aliyu Zurmi
July 19, 2023

Jami'an tsaron kasar Kenya sun kama sama da masu zanga-zanga 300, bayan da al'ummar kasar suka fantsama tituna suna boren adawa da halin matsin rayuwa da suke ciki a cewar ma'aikatar cikin gida.

https://p.dw.com/p/4U95t
Unruhen in Kenia
Hoto: Luis Tato/AFP

Madugun adawa Raila Odinga ya jagoranci ire-iren wadannan boren tun daga watan Maris inda ya ke kalubalantar gwamnati a kan halin da kasar ke ciki.

Ministan harkokin cikin gida Kithure Kindiki ya ce masu boren sun far fasa shaguna da kona gine-ginen gwamnati. 

Shugban kasar Kenya William Ruto a ziyarar da ya kai yankin Kericho ya bayyana cewar kasar ba ta bukatar yamutsi da tashin hankali.

Mahukuntan Kenya na zargin madugun adawa da da rura wutar rikicin da ke neman barkewa a kasar.