An kama waɗanda suka kai hare-hare a Yuganda
August 12, 2010Talla
Hukumomi a ƙasar Yuganda sun bada sanarwa cewa sun capke dukanin mutane da suka yi yunƙurin kai hare hare a ƙasar a cikin watan jiya.A wani taron manema labarai da ya kira shugaban hukumar leken asiri na ƙasar, James Mugira ya ce sun kama mutane huɗu dukaninsu yan ƙasar Ruwanda waɗanda suka aikata ta'asar.
Sannan kuma ya bayyana cewa yanzu haka sun dage wajan ci-gaba da farautar yan ta'addar.A ranar 11 ga watan yuli da ya gabata ne dai wasu mutane suka kai wasu tagwayyen hare hare a birni Kampala wanda a cikinsa mutane 76 suka rasa rayukansu,
Hare-haren kuwa wanda daga bisanni ƙungiyar al-shabab ta ƙasar Somaliya ta yi ikirarin kaiwa
Mawallafi :Abdourahamane Hassane.
Edita : Zainab Mohammed Abubakar