An kame Mbabazi da ke kalubalantar shugaba Museveni
July 9, 2015Talla
'Yan sanda a Yuganda sun kame tsohon Firaministan kasar Patrick Amama Mbabazi da ke shirin kalubalantar Shugaba Yoweri Museveni a zaben shekarar 2016.
Lauyansa ya ce an tsare Mista Mbabazi a garin Njeru mai tazarar kilomita 80 gabas da Kampala babban birnin kasar, lokacin da yake kan hanyar halartar wani gangamin.
'Yan sanda sun ce gangamin da Mista Mbabazi ke shirin yi wa jawabi, haramtacce ne. Wani kakakin 'yan sanda ya ce yanzu haka ana tsare da Mbabazi a wani caj ofis da ke birnin Kampala, kuma za a sako shi ba da wata tuhuma ba.
Ana yi wa Mbabazi kallon daya daga cikin jigajigan mutane a Yuganda kafin shugaba Museveni ya kore shi daga mukamin Firaminista a bara, bisa zargin nuna sha'awar zama shugaban kasa.