1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kammala taron ministocin kudi na kungiyar G7 a birnin London

December 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvIC

An kammala shawarwarin yini biyu na ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kungiyar kasashen duniya mafi arziki wato G7 a birnin London. A cikin sanarwar bayan taron da ta bayar kungiyar ta G7 ta yi kira ga sauran kasashen da zasu halarci taron kungiyar cinikaiya ta duniya da za´a yi a Hongkong a tsakiyar wannan wata da su taimaka a kara bude kofofin kasuwannin duniya. Bisa ga dukkan alamu dai wannan kira tamkar hannunka mai sanda ne ga kasashe masu tasowa, wadanda suka ce ba zasu bude kofofin kasuwanninsu ga kasashe masu arziki ba, har sai an rage kudaden tallafi da na fito akan kayan amfanin gona. Kungiyar ta G7 ta ce ta na sa rai tattalin duniya zai samu bunkasa amma tashin farashin man fetir na janyo tafiyar hawainiya.