Lagos: Martani kan dokar zaman gida
April 14, 2020A jawabinsa Shugaba Muhammadu Buharin ya ce, jihohin na Lagos da Ogun da kuma Abuja babban birnin Tarayyar Najeriyar, za su ci gab da kasancewa karkashin dokar zaman gida har nan da tsawon makonni biyu.
Hakan dai ya biyo bayan yadda biranen uku suka kasance na kan gaba a yawan masu dauke da cutar Coronavirus da ta addabi duniya kuma ta ke saurin yaduwa.
Matakan dakile yaduwar cutar
Da take jawabi kan tsawaita dokar, kwamishiniyar lafiya ta jihar Ogun Dr Tomi Coker cewa ta yi: "Babban abin da muka sanya a gaba shi ne hana cakuduwa da alumma, domin bincike ya tabbatar ta haka ne ake yada cutar a gari, shi ya sanya muke goyan bayan zama a gida tun kafin batun yafi karfinmu."
Sai dai a hannu guda kungiyar Human Rights Watch ta fitar da wata sanarwa, inda ta soki matakin shugaban kasar na karin wa'adin zaman gidan har zuwa nan da makonni biyu ba tare da an saar da wadataccen abinci da ruwan sha da sauran bukatu na rayuwa ba.
Hargitsi a jihar Lagos
A jawabin Shugaba Buharin ya jinjinawa sarakuna bisa gudummawar da suke bayarwa domin yaki da cutar. An dai sami 'yar hatsaniya a Lagos daga wasu sassan jihar, inda matasa su kai ta hargowa wanda nan take kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Lagos Mr Odumusu Hakeem ya yi wa tufkar hanci.