An karrama 'yan Afirka bisa kokarinsu na kare muhalli
May 23, 2018Shekaru 44 Gerald Bigurube mai shekaru 66 dan kasar Tanzaniya ya sadaukar don ganin dabbobin dawan dake kasarsa ta Tanzaniya da kuma muhalli sun tsira daga barazanar da suke fuskanta a nahiyar Afrika baki daya, a matsayinsa na dadadden shugaban hukumar kula da gidan ajiyar dabbobin kasar watau TANAPA, ya jagoranci yaki da fataucin hauren giwa, ya kasance daya daga cikin wadanda suka shige gaba wajen tabbatar da ingantar gandun daji da muhalli a Tanzaniya har sai da kasar ta yi nasarar samun makudan kudade a fannin 'yan yawon bude ido.
Shi kuwa Clovis Razafimalala na kasar Madagaska ya shiga harkar tsare gandun daji da muhallin ne daga baya inda ya yi shura wajen ganin dazuzzukan dake kasar Madagaska sun tsira daga barazanar da ke illata su, sakamkon wannan gudummwa da wadannan mutane suka bayar a bana, gungun jagororin gidauniyar kasar Jamus a Afrika wacce ta kunshi wasu kwararru a fanni daban daban na duniya suka zabesu don samun lambar girmamawa ta Gidauniyar.
Koyaushe ana son samun wadanda za su kare muhalli tun daga tushe, mutanen da ke kishin kare dazuka kasashensu. Wannan ba shi bane karon farko da ake karrama 'yan asalin Afrika da lambar girmamawa ta kasar Jamus ba, don kuwa 'yan kasashe kamar Yuganda da Afirka ta Kudu gami da Tunisiya sun taba samun lambar a baya.