1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wasu daliban jami'ar Greenfield

Mouhamadou Awal Balarabe
April 23, 2021

'Yan bindiga da suka sace daliban jami'ar Greenfield a jihar Kadunan Najeriya sun kashe uku daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, a wasu hare-hare da aka kai a wata jihar da ke makwabtaka da ita.

https://p.dw.com/p/3sVM6
Entführung nigerianische Studenten in Kaduna
Hoto: Bosan Yakusak /REUTERS

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na Jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya sanar cewa 'yan fashi sun kashe dalibai uku, yayin da wasu kauyawa suka gamu da ajalinsu a abin da ya danganta da "aikin rashin imani".

Tun yammacin ranar Talata ne 'yan fashi suka mamaye jami’ar Greenfield a Kaduna, inda suka yi awon gaba da dalibai kimanin 20, a cewar wasu majiyoyi a cikin jami'ar da ba sa son a bayyana sunansu. Kuma an kashe wani ma'aikaci yayin harin. Sai dai har yanzu hukumomi a jihar Kaduna ba su bayyana ainihin adadin daliban da aka sace ba.

'Yan fashi da makamai sun yi kaurin suna wajen satar dabbobi tare da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa a yankunan Kudu maso Yamma da kuma Arewa maso yammacin Najeriya. Yara 'yan makaranta 730 ne aka sace tun daga watan Disamba ya zuwa yanzu a arewacin kasar.