1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta rabu da Polio kwata-kwata

Abbany Zulfikar AH
August 25, 2020

Nahiyar Afirka ta yi ban kwana da cutar Polio wato shan Inna, sai dai da alama har' yanzu da sauran rina a kaba na yadda za a yaki cutar a kasashen Pakistan da Afganistan da suka rage da ita a duniya.

https://p.dw.com/p/3hV0o
Nigeria Polio Virus Impfung
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Wolfe

Fatan da aka dade da shi a duniya shi ne na kawar da cutar Polio wato shan inna daga Afirka, inda Najeriya ta zama kasa ta karshe a Afirka da ta kakkabe cutar. Wata hukuma mai zaman kan ta da ke sa ido kan cutar Polio ta kasa da kasa, ta ayyana ficewar Najeriya cikin jerin kasashen da babu Polio bayan rashin samun mai dauke da cutar tsawon shekaru uku. To sai dai akwai bukatar yin hattara, a cewar Farfeser David L. Heymann na makarantar nazarin kiwon lafiya da cututtuka masu yaduwa a yankuna masu zafi ta birnin Landan: “Ba za a iya yin hasashen girmar hatsarin ba, amma akwai hatsari muddin cutar Polio ta rage wasu sassan duniya, akwai barazanar ta sake yaduwa tsakanin mutane zuwa ko'ina. Saboda haka, yana wuya a iya hasashe a yanzu, abin da muke son maida hankali shi ne Afganistan da Pakistan sun yaki cutar su ma ta yadda duniyar za ta zama ba cutar.”

Akwai sauran rina a kaba a Pakistan da Afganistan inda cutar Polio ba ta  kau ba
Yaki da cututtuka abu ne mai matukar wahalar gaske, zuwa yanzu dai cututtukan kurajen fata da cutar dabbobi su ne cututtuka biyu da aka iya kawar da su a doron duniya. To ko wani mataki ya dace a dauka gaba ganin har' yanzu kasashen Pakistan da Afganistan sun rage da cutar? Ga abin da Farfeser David L  Heymann ke cewa: ''A gaskiya abin da za a bukata shi ne ci gaba da rigakafin kariya na hana yaduwar cutar, a lokaci guda kuma a rika sa ido kan tsare-tsaren da suke kasa a ko'ina, saboda tabbatar da yaki da cutar a duniya na nufin sai in kowace kasa ta tabbatar ba wanda ya sake kamuwa da cutar na tsawon shekaru uku.”

Pakistan Polio Impfung
Hoto: Getty Images/AFP/F. Naeem

Kara daukar matakai dangane da yaki da cutar Polio a wasu kasashen duniya
Sama da Euro biliyan 18 aka kashe a kokarin kawar da cutar Polio, amma duk da haka da sauran tafiya. Matakin da kwararrun ke ganin akwai bukatar sake fasalta tsarin da ake bi na dakile cututtuka. Cutar Polio ta zama barazana ga duniya, cutar da ta nakasa dubban yara a duniya ta kuma yi sanadiyyar mutuwar wasu da dama. An fara samun rigakafin cutar a shekarun 1960 zuwa  19 70 kafin ta sake barkewa a duniya a shekarar ta 1980, a lokacin an kiyasta sama da mutane dubu 350 cutar ke shanye wa barin jiki a duk shekara cikin kasashe 125. 

Syrien | WHO Polio Impfung
Hoto: picture-alliance/dpa/ZUMAPRESS