An kawo karshe dokar hana fita a Saliyo
September 22, 2014Talla
Hukumomi dai sun ce wannan matakin da suka dauka ya taimaka musu matuka wajen gano wanda suka kamu da cutar kuma ba su je asibiti don neman magani ba, yayin da suka ce sun samu damar ganowa tare da binne gawarwakin kimanin mutane 70 wadda cutar ta Ebola ta yi ajalinsu.
To sai dai duk da wannan nasarar da gwamnatin kasar ta ce ta samu, a hannu guda wasu al'ummar kasar da masu sanya idanu kan shirin da ya gudana sun ce irin aikin da jami'an kiwon lafiya na sa kai suka yi yayin da aka sanya dokar basu gamasar da su ba.
Saliyo dai na daga cikin kasashen yammacin Afirka da cutar Ebola ta bulla kuma aka samu asarar rayukan jama'a da dama.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal