1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen rikici a kasar Kenya

November 25, 2013

Jami'an 'yan sanda a Kenya sun ce zaman lafiya ya dawo kamar yadda yake a baya, a kauyen Lorokon da ya sha fama da fadan kabilanci.

https://p.dw.com/p/1AOYV
Hoto: Getty Images/AFP

A makon da ya gabata ne dai wasu 'yan bindiga dauke da makamai, suka yiwa kauyen Lorokon dake yankin arewa maso yammacin kasar, da kuma ya kasance gari ga 'yan kabilar Pokot da Turkana da basa ga maciji da juna dirar mikiya.

'Yan binigar dai sun kwace ofisoshin 'yan sanda uku tare kuma da yin fito na fito da jami'an 'yan sanda dauke da manyan makamai da aka tura domin shawo kan rikicin.

Rahotannin sun bayyana cewa fada a wannan kauye ba wani sabon abu bane kasancewar an saba yinsa bisa dalilai na fada tsakanin manoma da makiyaya. Haka nan ma ana fama da fada akan filaye a tsakanin kabilun na Pokot da kuma Turkana.

Maawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Auwal Balarabe