An kawo karshen zanga zanga a Kashmir
May 14, 2024Talla
Masu zanga zanga a yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan sun dakatar da gangamin da suke yi bayan da wadanda suka shirya zanga zangar suka amince da tayin tallafi da kuma rage farashin kayayyaki da gwamnati ta yi musu.
Pakistan da Indiya kowannensu na iko da wani bangare na yankin na Himalaya amma kuma suna ikrarin dukkan yankin na su ne.
Yankin ya kasance abin da ya dade yana haifar da takaddama tsakanin kasashen biyu da suka mallaki makamin nukiliya wadanda kuma suka gwabza yaki da juna har sau uku akan yankin.
Yankin Kashmir da ke karkashin iko Pakistan ya kasu zuwa rassa uku masu kwarya kwaryar cin gashin kai wadanda a hukumance ake kira Azad Kashmir da kuma yankin da ke karkashin ikon tarayya mai suna Gilgit-Baltistan.