1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe kungiyar Real Madrid saboda Coronavirus

March 12, 2020

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Spain za ta fusaknci kebewa da gwaji a kan cutar Coranvirus bayan wani dan wasa ya kamu da cutar.

https://p.dw.com/p/3ZHyW
Fußball Champions League Team Real Madrid
Hoto: picture-alliance/empics/N. Potts

A wata sanarwa da ta fito daga mahukumtan kungiyar a ranar Alhamis, an ruwaito jami'an kungiyar na cewa daukar wannan mataki ya zama wajibi domin an samu wani cikin 'yan wasan kungiyar da ke bangaren kwallon hannu ya kamu da cutar. Sanarwar ta ce ganin irin cudanyar da aka yi da shi ana zullumin wasu ma za su iya kamuwa. A don haka za a kebe su don gano ko sun kamu da cutar. Wannan mataki na kungiyar Real Madrid na zuwa ne bayan 'yan wasu sa'o'i da mahukumtan La liga mai shirya wasannin kwallon kafa a Spain suka sanar da rufe duk wasu harkokin wasanni na makonni biyu. Kawo yanzu dai Spain wace ta dauki wannan mataki a baya-bayan nan na da mutane 2,140 wadanda suka kamu da cutar Coronavirus yayin da kuma mutane 48 suka mutu a sakamakon cutar.