1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta koma tattaunawa da Taliban

Suleiman Babayo USU
November 29, 2019

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce an sake komawa kan teburin tattauna da kungiyar Taliban ta Afghanistan mai dauke da makamai yayin ziyarar ba zata da ya kai kasar.

https://p.dw.com/p/3TvHP
Afghanistan | Donald Trump besucht Truppen zu Thanskgiving
Hoto: Getty Imags/AFP/O. Douliery

A wannan Alhamis da ta gabata Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce an sake komawa kan teburin tattauna da kungiyar Taliban ta Afghanistan mai dauke da makamai. Shugaban ya bayyana haka yayin ziyarar ba zata ga dakarun Amirka da ke kasar ta Afghanistan domin shagulgular bikin Thanksgiving. Akwai kimanin dakarun Amirka 12,000 da ke kasar ta Afghanistan.

Yayin ziyarar Shugaba Trump na Amirka ya shafwe kimanin sa'o'i uku na gani halin da sojojin ke ciki sannan kuma ya zauna tare da Shugaba Ashraf Ghani na kasar ta Afghanistan kan hanyoyin magance rikice-rikicen da ake samu a kasar inda ya kawo karshen ziyarar cikin dare.