An kori shugabar hukumar EFCC Farida Waziri
November 23, 2011A wani mataki na ba zato ba tsammani shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sallami shugabar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC Farida Waziri. Dama dai an sha sukar Farida Waziri da cewa wasu 'yan siyasa mahukunktan ƙasar ne ke juya akalarta. Kakakin hukumar ta EFCC Femi Babafemi wanda ya tabbatar da sallamar Farida Waziri yace ba shi da masaniya kan dalilin da ya sa shugaban ƙasar ya kore ta. An dai kafa hukumar ta EFCC ce 'yan shekaru kaɗan bayan da Najeriya ta koma tafarkin dimokraɗiyya a shekarar 1999. Shugaban hukumar na farko Malam Nuhu Ribadu ya yi iƙrarin cewa Najeriya ta yi hasarar maƙudan kuɗaɗe da yawansu ya kai Dala biliyan 380 a cin hanci da rashawa tsakanin shekarun 1960 zuwa 1999. A yanzu haka dai an naɗa Alhaji Ibrahim Lamurde domin ya maye gurbin Farida waziri a matsayin sabon shugaban riƙo na hukumar ta EFCC.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmad Tijani Lawal