1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori shugabar hukumar EFCC

November 23, 2011

Gwamanatin Tarrayar Najeriya ta sanar da salamar shugabar hukumar yaƙi da yi wa arzikin ƙasar ta'ananti ba tare da baiyana wasu dalilai ba

https://p.dw.com/p/13Fe8
Goodluck Jonathan shugaban ƙasar Tarrayar NajeriyaHoto: AP

A wani abinda ka iya yin tasiri ga yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, gwamnatin ƙasar ta sanar cire shugabar hukumar yaƙi da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa wato EFFC Mrs Faraida Waziri, bayan dadaewa da aka yi ana koken ƙaruwar matasalar cin hanci .

Gwamnatin ba ta baiyana dalilan salamar shugabar hukumar ta EFCC

Sanarwar sauke shugabar hukumar ta EFFC Farida Waziri wacce ke ƙunshe a sanarwar da mai bai wa shugaban Najeriya shawara a fanin yaɗa labaru Reuben Abati ya bayar ta baiyana naɗa Ibrahim Lamorde a matsayin muƙadashin shugaban hukumar ta EFCC, wanda dama can ya taɓa riƙe wannan muƙami kafin naɗa Mrs Waziri. To sai dai ba'a bayyana dalilan sauketa ba daga muƙamin.

Tsohuwar shugabar hukumar ta EFCC, ta fuskanci suka sosai na rashin kazar-kazar a harkar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, saboda abinda ake ganin cusa siyasa ne a cikin aikin, lamarin da ya a sanya ƙaruwar matsalar. Malam Awwal Musa Rafsanjani na kungiyar CICILAC da suke fafutukar yaƙi da cin hanci da rasahawa a Najeriyar ya baiyana cewa wannan mataki na iya yin tasiri a harkar yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar wanda ake ganin wannan muhimmin ci gaba ne..

Karte Nigeria mit Hauptstadt Abuja Englisch Deutsch
Taswirar Najeriya

Ko da ya ke tsohuwar shugabar hukumar ta EFCC ta sha koken cewa kotuna Najeriya ne ke kawo mata cikas, to sai dai naɗa Ibrahin Lamorde da dama ya san cike da waje na batun wannan hukuma ta EFCC ya sanya tambayar ko wannan mataki na iya sa ran samun sauyi daga matsalar? Malam Abubakar Ali mai sharhi ne a fanin al'ammuran yau da kullum a Najeriya.

Tsohuwar shugabar hukumar ta EFCC ta ce kotun ce ke kawo ma ta cikas wajan gudanar da aikin ta

Zargin cusa siyasa a cikin harakar cin hancin da rashawa dai na daga cikin matsalolin da ke haifar da koma baya a harakar, inda matsalar ta yi katutu baga ma'aikatan gwamnati ba har ma a kamfanoni masu zaman kansu, yan kasuwa da a makanrantun ƙasar. Ko da a watan Augustan da ya gabata sai da a hukumar kare hakin jama'a ta baiyana cewar batun cin hanci da rashawa ya ja baya sosai a Najeriyar saboda abinda ta baiyana da zagon ƙasar da ya ke fuskanta daga ɓangarori da dama. A yanzu za'a sa ido a ga tasirin da wannan sauyi ka iya yi, don sanin ko gwamnati da gaske ta ke batun cin hanci da rashawa a Najeriyar.

Mawallafi :Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani