Jamus: An kwace lasisin malamin Musulunci
June 26, 2021Kawo yanzu dai gidauniyar da ke da ikon tantance maluman addinin Islama a jihar Baden-Württemberg da ke kudu maso gabashin Jamus ba ta zayyana dalilanta na karbe shaidar malumtar daga hannun malamin ba. Sai dai wata Bajamushiya mai bincike a kan addinin Musulumci Susanne Schröter ta yi zargin gidauniyar ta kwace wa malamin lasisi ne saboda sassaucin da yake da shi a cikin fatawowinsa na Musulumci wadanda ke cin karo da fatawowin sauran malaman da ake wa kallon masu tsattsauran ra'ayi ne.
Malam Abdel-Hakim dai ya wallafa wani littafi a baya wanda ya haddasa cece-kuce a tsakanin masana Musulumci a Jamus, inda a cikin littafin ya nuna cewa mata Musulmai ba sa bukatar sanya hijabi idan za su fita waje ko za su shiga bainar jama'a.
A hirarsa da jaridar Jamus ta Die Welt, malamin ya yi zargin cewa an kwace masa lasisin malumtarsa ta Musulumci ne saboda yadda yake tallata Musulumci mai sauki ga jama'a. A yanzu dai malamin na da ikon shigar da kara don bukatar dawo masa da lasisin.