An rantsar da sabon sarki a kasar Japan
May 1, 2019Talla
Manyan baki da yawansu ya kai 290 ne suka halarci bikin nadin sabon sarki Naruhito ciki kuwa harda Firaiminista Shinzo Abe da daukacin iyalan masarautar. Sarkin na 126 a masarautar kuma tsohon dalibin jami'ar Oxford ya rantse zai gudanar da shugabanci kamar yadda magabatansa suka yi .
Masarautar ta Japan kuma guda cikin fitattaun masarautun duniya na da wata tsohuwar al'ada wacce ta haramta wa mata halaratar gurin rantsar da sabon sarki. Al'ummar kasar Japan sun shaidi sarki Akihito mai murabus da hakuri da tabbatar da zaman lafiya da kuma shiga a dama da shi a lokutan farin ciki da na juyayi,