An sa ranar gurfanar da shugabannin ƙungiyar 'Yan uwa Musulmi a gaban kuliya
August 4, 2013A wannan lahadin ne wata Kotu a Masar ta sanya ranar da jagororin ƙungiyar 'Yan uwa Musulmi zasu gurfana a gaban ƙuliya, a wani matakin da ake hangen zai iya harzuƙa magoya bayan hamɓararren shugaba Mohammad Mursi.
Wannan ya zo ne daura da ganawar muƙadashin sakataren kula da harkokin wajen Amirka William Burns da shugaban rundunar sojin ƙasar Abdel Fatah al-Sisi a wani yunƙuri na gano bakin zaren warware rikicin siyasar ƙasar.
Jagorar ƙungiyar ta 'yan uwa musulmi Mohammad Badie wanda a yanzu haka yake ɓuya da mataimakansa biyu Khairat al Shater da Rashad Bayoumi waɗanda ke gidan kason Tora da ke Alƙahira na fuskanatar zargin harzuƙa mutane wajen janyo tashe-tashen hankulan da yayi sanadiyyar rayukan wasu.
Za su gurfana a gaban kuliyar ne ranar 25 ga wannan wata na Ogosta tare da wasu 'yan ƙungiyar uku waɗanda ake zargi da kashe masu zanga-zanga
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu Usman