1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sallami shugaban hukumar EFCC

Zainab MohammedDecember 28, 2007
https://p.dw.com/p/ChUS

Shugaban Rundunar ‚yansanda a tarayyar Nigeria Mike Okiro,ya sanar da tura shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashwa ta EFCC Nuhu Ribadu,zuwa cibiyar nazarin harkokin tsaro na shekara guda a jihar Plateau.Wannan dai manazarta kann lamuran kasa sun bayyana shi da kasancewa,wani yunkuri ne na karya marta bar Nigeriar,wadda ta taka rawa wajen yaki da rashwa a karkashin hukumar ta EFCC:Mai bincike kann Nigeria dake kungiyar kare hakkin jamaa ta human right WatchChris Albin-Lackey,yace barin wannan hukuma da Ribadu zai yi,tamkar wani mayar da hannun agogo baya ne dangane dangane da harkokin rashawa a Nigeria.Shugaba Umaru Musa ‚Yar Adua,wadda ofiyhinsa ce keda alhakin kirkiro wannan hukuma a ta EFCC akarkashin doka,baice komai kawo yanzu dangane da wannan batu.