An nada sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya
January 26, 2021Bayan share tsawon lokaci ana jira, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya sauke manyan hafsoshin tsaron kasar tare da maye gurbinsu da sababbabi fil.
A baya dai an musu kirari irin na dashi mai rai guda tara, sun kuma zamo hafsoshi mafi dadewa bisa mulki a cikin tarihin sojan kasar tun bayan yanci.
Kafin wata sabuwar sanarwa ta ba zato ba tsamanni da ta yi tafiyar ruwa da daukacin manyan hafsoshi na kasar.
Sanarwar da fadar gwamnatin ta fitar dai ta kuma ambato Manjor janar Leo Irabor a matsayin babban hafsan tsaron kasar a yayin kuma da Manjor Janar Ibrahim Attahir zai shugabanci hafsoshi na kasa na kasar.
Sanarwar ta kuma ce shugaba Buhari ya nada Real Admiral A. Z. Gambo domin shugabantar rundunar ruwa a yayin kuma da Air Vice Marshal A.O. Amao ke zaman shugaban sojan sama.
Kafin sabuwar sanarwar dai shugaba Buhari ya fuskanci matsin lamba game da bukatar sauyin hafsoshin walau daga talakawan kasa ya zuwa su kansu masu takama da siyasar ta.
To sai dai kuma a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin gwamnatin ta Abujar jan kafa ta shugaban kasar na da ruwa da tsaki da ilimi na shi kadai game da hali na tsaron cikin kasar.
Malam Lamiri mai gani har hanji ko kuma jan kafa cikin mulki na kasa dai akalla biyu cikin sabbabin hafsoshin dai ba baki ba ne cikin rikicin tsaron da tarrayar Najeriyar ke fuskanta yanzu.
Janar Leo Irabor da shi kansa Janar Ibrahim Attahiru dai sun share lokaci su na jagorantar rundunar sojojin JTF da ke yakin Boko ta haramun a sashen Arewa maso Gabas.
Kuma a fadar Captain Abdullahi Bakoji mai ritaya da ke sharhi a cikin harkar sojan, sabbabin hafsoshin su na da babban ilimi a cikin yakin ta'adancin kasar da yaki ci ya kuma ki cinyewa.
To sai dai kuma in har sabuwar sanarwar tana shirin dadada rai na 'yan kasar da daman gaske, da kyar da gumin goshi ta kai ga biya na bukata a fadar Kabir Adamu dake zaman masani na tsaron cikin kasar.
Abun jira a gani dai na zaman sabuwar rawar takawa ga sabbabin hafsoshin da ke da jan aikin sauya da dama a lokaci na kankane cikin tsarin tsaron kasar da ke lalace.