An samar da makuden kudi na dakile cutar Mpox a Afirka
September 13, 2024Talla
Cutar kyandar biri ko kuma Mpox wacce aka gano bullar ta a kasashen Afirka kusan 15, ta fi kamari ne a kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Burundi da Kwango Brazzaville da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A farkon watan Augustan da ya gabata ne Hukumar Lafiya ta MDD ta ayyana cutar a matsayin wata babbar barazana ga duniya, wanda kuma ta bukaci a gagauta samar da rigakafi domin dakile ta.
Sama da mutane 26,000 ne cutar ta kama a kasashe daban-daban a nahiyar Afirka yayin da ta yi kuma ajalin mutane sama da 720. Kashen duniya na ci gaba da kai dauki ga Afirka na ganin an shawo kan cutar cikin hanzari.
Karin Bayani: Jamus za ta bai wa Afirka rigakafin cutar Kyandar Biri