LafiyaNa duniya
WHO: Bullar sabon nau'in corona
August 18, 2023Talla
Hukumomi biyu sun ce sun yanke shawarar gudanar da bincike domin rabe bambance-bambancen da ke akwai tsakanin sabon nau'in kwayar cutar da suka yi wa lakabi da BA.2.86 da wancan na baya, la'akari da adadi mai yawa na kwayoyi masu saurin ninkawa da ya kunsa wadanda yawansu ya haura maki 30. Da ma dai a wani rohoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar a baya-bayan nan, ta ce a tsukin 17 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Agusta na wannan shekarar an samu mutane miliyan guda da dubu 400 da suka kamu da cutar COVID-19. Cikin wannan adadi dai, mutane dubu biyu da 300 suka bakunci lahira. Adadin na nuni da cewa tun bayan lafawar annobar, an samu karuwar masu kamuwa da ita da kaso 63 cikin 100.