An samu karuwar aikata fyade a Indiya
January 2, 2015Talla
A wani taro da ya saba yi da manema labarai duk shekara kwamishin 'yan sandan na New Delhi din Bhim Sain Bassi ya ce a watanni 12 da suka gabata sun karbi korafi na fyade kimanin 2,069 a birnin kadai wanda ke zaman karin kashi 31.6 cikin 100 idan aka kwatanta hakan da shekara ta 2013.
To sai dai duk da karin adadin wadanda ake yi wa fyade, Mr. Bassi ya ce hakan ba ya na nufin birnin na kara zama mai hadarin gaske ga mata, hasalima ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kawar da wannan mummunar ta'ada baki daya.
A 'yan shekarun da suka gabata fyade dai ya zama ruwan dare a New Delhi da sauran sassan kasar, batun da kungiyoyin mata da na kare hakkin bani adama ke cigaba da nuna damuwarsu a kai.