Kocin Uganda zai yi shekaru 3 a kurkuku
October 19, 2021A watan Disamban shekarar 2020 ne Sredojevic ya aikata laifukan da aka yanke masa hukunci, lokacin da yake horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Zambiya, inda wata mata mai shekaru 39 mai raba gahawa "coffee" a filin wasa a Afirka ta Kudu, ta tambayi Sredojevic ko ya dauki sukari, sai ya ce "a a kuma ya kara da cewa "ina bukatar wani nau'in sukari", yana nuna al'aurarta. Daga baya a ranar da abin ya faru, ya sake taba mata jiki ta hanyar da ba ta dace ba.
A watan Yulin 2021 hukumar kwallon kafa ta kasar Uganda, ta sake nada Sredojevic dan asalin kasar Sabiya a matsayin kocin kungiyar "Cranes" bayan barin kungiyar shekaru hudu da suka gabata kan takkadamar kudade dala 54,000 na albashi da ba a biya ba.
Yanzu haka yana kan kwantiragin shekaru uku, don shiga wasannin share fage na shiga gasar cin kofin duniya da za a kara a Katar a 2022. Tun a shekarar 2001 Milutin Sredojevic yana horar da kungiyoyin kwallon kafa na kasashe da dama a nahiyar Afirka.