1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kama hanyar sulhunta 'yan Taliban da Afghanistan

Abdoulaye Mamane Amadou
July 9, 2019

A wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Katar ta bayyana cewa an samu nasara kan tattauna shirin zaman lafiyar kasar Afghanistan da aka gudanar acikin wannan makon.

https://p.dw.com/p/3LmDo
Doha  Intra Afghan Dialogue Afghanistan Konferenz
Hoto: AFP/K. Jaafar

Sanarwar wadda aka fitar a wannan Talatar ta yi nuni da cewa ana samun nasara kuma za a samu wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin bangarorin da suka tattauna shirin zaman lafiyar na Afghanistan, kamar yadda jakada na musamman na kasar ta Katar kan shirin zaman lafiyar Afghanistan Mutlaq bin Majid Al Qahtan ya tabbatar a cikin sanarwar.

Manya-manyan masu ruwa da tsaki a kasar Afghanistan suka koma kan teburin sulhu da mayakan na Taliban a birnin Doha, da nufin kawo karshen rikicin shekaru 18 da ya lakume dubban rayuka da dukiyoyi da dama.