1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu nasara a taron muhalli na Lima

Ahmed SalisuDecember 12, 2014

Manyan kasashen duniya sun hada kai da takwarorinsu masu tasowa wajen cimma matsaya kan hanyoyi tinkarar matsayar sauyin yanayi a taron birnin Paris a 2015.

https://p.dw.com/p/1E3Dw
Hoto: Getty Images/C. Bouronclea

Taron dai ya hada kan manyan jami'an gwamnatocin kasahsen duniya da kungiyoyin da aiyyuka wajen inganta muhalli da kuma masu rajin kiyaye muhalli inda suka tattauna kan batutuwa da dama. To sai dai rahotanni na nuna cewar kamar kwalliya ba ta kai ga biyan kudin sabulu ba, musamman ma idan aka danganta abun da babban taron da za a yi a badi a birnin Paris kan sauya yarjejeniyar nan ta Kyoto game da inganta muhalli da kuma rage dumamar yanayi.

Peru Klimakonferenz in Lima COP 20 John Kerry bei Ollanta Humala
Hoto: Reuters/E. Castro-Mendivil

To sai dai duk da haka masana muhalli da ma masu rajin kare shi na ganin abu ne mai wahala kasashen duniya su iya kaiwa ga cimma burin da aka sanya gaba kamar yadda ya ke kunshe a cikin muradin Majalisar Dinkin Duniya na kaiwa ga rage dumamar yanayi zuwa digiri biyu a ma'aunin celcius. Wani babban batu da ke zaman kalubale ga kaiwa matsayin da ake so shi ne yadda kasashen za su bada gudumawarsu wajen kaiwa ga rage dumamar yanayi musamman ma irin kokarin da ya kamata a ce kowacce kasa ta yi duba da irin cigaban da ta ke da shi da ma karfinta na yin hakan.

Barbara Hendricks UN Klimakonferenz Lima 11.12.2014
Hoto: picture-alliance/epa/P. Aguilar

Baya ga wannan, wani abu da ake kallo a matsayin gibi a tafiyar da ake yi shi ne irin korafin da wakilan nahiyar Afirka suka yi wajen taron inda suke cewar ba a bada muhimmanci ga irin bukatun da suka gabatar wajen taron ba duk kuwa da irin hobbasa din da Oxafam ta yi na bada kudaden da wasunsu ke bukata wajen yakar tabarbarewar muhalli. Abin jira a gani dai shi ne irin matakan da shugabannin kasashen duniya za su dauka nan da watanni 12 da ke tafe da nufin shata sabuwar hanya ta yi wa muhalli garkuwa daga irin kalubalen da yake fuskantarsa.