An samu zabtarewar ƙasa a Japan
August 20, 2014Talla
Kimanin mutane 36 da suka hada da yara sun hallaka sakamakon zabtarewar ƙasa bayan ruwan sama da aka sheka a yankin yammacin birnin Hiroshima na ƙasar Japan.'Yan sanda sun ce akwai yiwuwar samun ƙarin mutanen da abin ya shafa, yayin da ake ci gaba da neman mutane bakwai da suka ɓace bayan faruwar lamarin. Masu aikin ceto sun yi amfani da jirage sama masu saukan ungulu domin kwashe mutanen da suka tsira.
Tuni aka tura da dakaru 500 domin aikin ceto, yayin da Firamnistan ƙasar ta Japan Shinzo Abe ya katse hutun da yake yi na lokacin bazara domin komawa Tokyo babban birnin ƙasar, domin tinkarar lamarin.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane