Chaina ta soke bikin sabuwar shekara
January 23, 2020Talla
Gwamnatin Chaina ta soke kasaitaccen bikin sabuwar shekara da aka saba gudanarwa a sakamakon bullar cutar Coronavirus da ake ta fadi tashin ganin an shawo kanta. A wannan Alhamis gwamnati ta sanar da soke bikin bayan da aka kwashi kwanaki ana kokarin ganin an shawo kan cutar.
Chaina ta dauki kwararran matakai na hana zirga zirga musanman na jirage da duk wasu taruka a sassan kasar bayan da cutar ta kama mutum sama da dari hudu, mutum goma sha bakwai ne aka tabbatar da sun mutu a sakamakon cutar ta Corona mai saurin kisa.