An soke izinin ziyarar Ban Ki Moon a Korea ta Arewa
May 20, 2015Wannan mataki dai ya biyo bayan wasu kalaman da Ban Ki Moon din ya yi, inda ya yi kira ga hukumomin na Korea ta Arewa da su kauracewa duk wani yanayi da zai kara tadda jijiyoyin wuya na fannin soja a yankin tsibirin kasar. Yayin da ya ke halartar wani babban zaman taro a kasar Korea ta Kudu ne, Ban Ki Moon din da kansa ya sanar cewa, da sanyin safiyar wannan Laraba ce ofishin diflomasiyyar kasar ta Korea ta Arewa ya sanar da shi cewa sun soke izinin da suka bashi na kai ziyara a kasar, ziyarar da ita ce irinta ta farko ta wani Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a wannan kasa tun shekaru 20 da suka gabata. Daga nashi bengare ofishin ministan da ke kula da harkokin kasashen na Korea da ke Korea da Kudu ya ce shi ma bai ji dadin wannan lamari ba.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu