1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tono wasu mutane hudu da rai a Kenya

Salissou BoukariMay 5, 2016

Masu aikin ceto sun samu nasarar ceto wasu mutane da ransu a karkashin baraguzan soron benen nan da ya fadi yau da kwanaki shida a birnin Nairobi.

https://p.dw.com/p/1IisA
Kenia Einsturz Gebäudekomplex - Rettungsarbeiten
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Da sanyin safiyar ranar Alhamis din nan dai an samu gano wata mace da ranta, sannan kuma da an sake gano wasu mutanen guda uku suma da rai, mace biyu da namiji daya a cewar shugaban 'yan sandan birnin Nairobi. Yayin da aka fito da wadannan mutane da ransu, jama'a da ke wurin ta kwashi tabi tare da nuna murna, inda nan take aka saka musu na'urar nan ta nunfashi ta iskar shaka ta oxygene kafin daga bisani a fice da su ya zuwa asibiti.

A cewar Pius Masai, shugaban ma'aikatar kula da annoba ta kasar Kenya, wannan rana babbar rana ce ta farin ciki a gare su ganin yadda suka samu fiddo wadannan mutane da sauran rai.