An tsaurara matakan tsaro a birnin London bayan kisan wani soja
May 23, 2013'Yan sanda a birnin London sun tsaurara matakan tsaro a kewayen barikokin Birtaniya bayan wani hari da aka kai a birnin ranar Laraba da yamma, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum guda. Gwamnatin kasar ta bayyana harin da cewa na ta'addanci ne. A ranar Laraba wasu matasa biyu bakar fata dauke da makamai suka kashe wani mutum da gwamnati ta ce sojan Birtaniya ne, a bayyanar jama'a a unguwar Woolwich dake kudu maso gabacin babban birnin na Birtaniyya. A dangane da wannan harin Firaministan Birtaniya David Cameron ya katse wata ziyarar da yake yi a Faransa, ya koma gida inda ya jagoranci wani taron gaggawa na kwamitin harkokin tsaron kasa, inda ya bayyana cewa.
"Da farko wannan kasa za ta dage a kan matsayinta na yaki da tsattsauran ra'ayi da kuma ta'addanci. Ba za mu mika wuya ga kowane irin nau'i na ta'addanci ba. Na biyu dukkan al'umar wannan kasa na da wannan ra'ayi, wannan hari ne a kan Birtaniya da salon rayuwarta, kuma hari ne na bijire wa Musulunci da al'ummar Musulmi dake ba da gagarumar gudunmawa don ci-gaban wannan kasa."
Wannan lamarin ya auku ne kwanaki uku gabanin wasan karshe na cin kofin zakarun kwallon kafar Turai na Champions League a London, inda za a kara tsakanin kulob din Jamusawa guda biyu.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu