Zimbabuwe: An saka ranar zabe
May 31, 2018A cewar wakilin DW da ke birnin Harare, wannan sanarwar da gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta fitar a jiya Laraba, kusan babu wata murna a bangaren talakawan kasar ta Zimbabuwe dake zama a ketare domin kuwa basu da damar kada kuri'a bisa dokokin kasar duk kuwa da samun sauyin gwamnati.
Wani hukuncin da kotun kolin kasar ya yanke a yammacin jiya Laraba, shi ne ya haramtawa daukacin 'yan kasar Zimbabuwe mazauna ketare kada kuri'a, har sai lokacin da aka yi wa dokokin zaben kasar kwaskwarima. Kawo yanzu dai a hukumance babu yawan alkaluman 'yan kasar Zimbabuwe da suke tsere daga kasar izuwa kasashen ketare sakamakon matsalolin siyasa da na tattalin arziki, amma ana kiyasin sama da 'yan Zimbabwe miliyan biyu ne ke zama a kasashen waje.
Shugaba Mnangagwa zai fafata da dan takarar babbar jam'iyar adawa ta MDC Nelson Chamisa wanda matashi dan shekaru 40. Kawo yanzu dai ba a san dalilan da suka sa aka hanawa 'yan kasar da ke zama ketare 'yancin yin zabe ba to amma akasarin jama'a rayoyinsu sun karkata kan cewa babban dalilin shi ne mafi yawan 'yan Zimbabuwe da ke zama a kasashen waje sun fi alaka ne da jam'iyar adawa.