An yaba da matakin da Majalisar Dinkin Duniya akan kasar Burma
December 3, 2005Amirka ta yabawa kuri´ar da kwamitin sulhu na MDD ya kada baya-bayan nan akan kasar Burma. Kwamitin sulhun dai ya yi kira da a yi bayanin halin siyasar wannan kasa a hukumance. Jakadan Amirka a MDD John Bolton ya bayyana halin da ake ciki a Burma da cewa ya tabarbare domin gwamnati a birnin Yangon na ci-gaba da tsare firsinoni siyasa kimanin dubu daya kana kuma ta tsawaita wa´adin daurin talala da take yiwa shugabar ´yan adawa Aung San Suu Khi a gida har tsawon watanni 6. A ranar alhamis da ta wuce wata kungiyar kare hakkin bil Adam a nahiyar Asiya ta ba da wani rahoto wanda a ciki ta zargi gwamnatin Burma da ganawa firsinonin siyasa azaba. A watan jiya babbar mashawartar MDD ta zartas da wani kuduri wanda a ciki ta yi tir da keta hakkin bil Adam a cikin kasar ta Burma.